Furar Danko 87

 




87


.........“Dada wane É—a ne zai yi fushi da iyayensa. Balle ma ke nasan baki da laifi akan wannan al'amarin sam.”


     “Naji daÉ—i da ka fahimci haka Sulaiman, dan babu ta yanda zan goya bayan bare sama da jikana. A yanzu haka koda akai min katanga da bibiyar halin da kuke ciki ban zauna ba, kuma nayi alÆ™awarin sai Mawaddat ta dawo hanun Tajuddeen matsayin mata dan bazan taÉ“a amsar waninsa ba”.


   Wani irin farin ciki ne ya ratsa Alh. Sulaiman, dama shi yasan Dadarsa na tare da su. Dada dake murmushin itama ta Æ™ara Æ™asa da murya da faÉ—in, “Labari ma mai da É—i......” Tsaf ta kwashe yanda sukai da Lulu ta sanar masa. Baima san sanda ya lailayo wata ashariya ya dire ba a gaban mahaifiyar tasa. Ya ce, “No wander naga yaron nan Yousuf nata rawan kai, ashe shegen shine ya Æ™ulla komai”.


     “Wlhy kuwa, nima abin ya girgizani Sulaiman. Amma ka kwantar min da hankalinka jibi da kaina zanje na É—akko Mawaddat ko yaron nan na yawo da ubansa a baya sai ya saketa”.


   “ALLAH ya barmin ke Dada ta”.


Ya faɗa cikin wani irin matsanancin farin ciki. Gaba ɗaya damuwarsa ta shafe ma. Bai iya dogon Zama ba a gidan bayan sun ɗan tattauna akan abinda ya samu Baba da ta bashi labari ya wuce gida kasancewar dare ya fara yi, yana tabbatar mata gobe idan ALLAH ya kaimu Tajuddeen zai zo ya gaidata, da dai ya ɗauki fushi bazai sake zuwa wajensu ba, amma yanzu zai lallasoshi, dan zai sanar masa ƙoƙarin da take masa. Sosai Dada taji daɗin hakan, dan ita kam ALLAH ya jarabceta da shegen ƙulafucin ƴaƴanta da ma jikokin duka. Sai dai kuma matan ƴaƴan nata da babu wanda ta ɗagema hula a rashin mutunci, juyasu take san ranta kamar waina a tanda kamar yanda ta kame ƴaƴan nata ram a hannu sai yanda tace musu, Alh. Sulaiman ɗin nema dai kan botsare mata a wasu lokutan dan shima dai halayyar tata ce ya ɗebo tsaf. Shiyyasa takanji shakkarsa duk da kasancewar itace ta haifesa, san nan tana sonshi sosai wannan a bayyane yake a wajen kowa ma, dan sam idan rashin mutuncinsa ya tashi ba raga mata yake ba tun ma yana ƙaraminsa, balle yanzu da yake jin ya gawurta da tumbatsa a gidan ta fanin dukiya da yin suna a cikin ƴaƴan nasu. Amma a kullum Dada bata ganin laifinsa sai ma bashi goyon baya da takeyi....


     __________★


    MatuÆ™ar tashin hankali Smart ya shiga a lokacin da ya fahimci halin da Lulu ke ciki. Ta sanÆ™ame masa babu alamar rai tattare da gangar jikinta, da Æ™yar tunanin zuba mata ruwa yazo masa a rai, sai dai koda ya shafa mata ruwan ma shiru kake ji. Gaba É—aya ruwan ya zazzage mata zuciyarsa na wani irin dokawa tamkar zata faso Æ™irjinsa ta fito waje. Wata irin zaburowa tai jikinta na jijjiga. A tsahon rayuwarsa baya jin ya taÉ“a fuskantar makamancin farin ciki da tashin hankali masu gogayya da juna irin haka. Duk yanda yake tunanin iya shawo kan matsalar hakan ya gagara, dan yanayin nata ya wuce dukkan tunani. Yasan idan yace zai É—auketa zuwa asibiti a wannan halin bazai ma iya driving ba, to yama manta motar su Amrah sun tafi da ita gida, dan haka ya shiga neman wayarsa. Da Æ™yar ya iya samota a Æ™asa harta fashe. Bai damu ba ya shiga neman Ahmad dan shine kawai yazo masa a rai. 


     Shigowar kiran ta saka Ahmad kwashewa da dariya, amma daya É—aga sai ya dake dan shi duk tunaninsa Smart ya gano ne. Sai dai kuma jin muryarsa ta saka gabansa faÉ—uwa. Da sauri ya ce, “Mawashi Are you okay?”.


   “I am not Ahmad. Ina cikin tashin hankali ka taimakeni kazo mukai Mawaddat asibiti, Ahmad akwai matsala wlhy na saka yarinyar mutane a masifa....”


    Sosai zuciyar Ahmad ta jijjiga, amma sai yay saurin tarar numfashin Smart da faÉ—in, “Kaga Aliyu dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, ka faÉ—amin mike faruwa ne. Ka sakani a tashin hankali nima....”


   Cikin Æ™araji Smart ya katsesa da “Mi kake son sani ne Ahmad!! Ina faÉ—a maka kazo muje asibiti kana gaya min na kwantar da hankalina na sanar maka mike faruwa?. Ahmad ka taimakeni karna rasata, bazan iya yafema kaina ba idan hakan ta kasance”. Ya Æ™are maganar cikin sanyin murya hawaye masu zafi na gangaro masa a karo na farko... 


       KaÉ—an ya rage Ahmad yin aman zuciyarsa. Muryarsa na rawa da daburcewa ya ce, “Ka.. ka yi haÆ™uri gani nan zuwa.” baima jira amsar Smart É—in ba ya miÆ™e tare da figar jallabiya ya saka. Karo suka kusan ci da Coach da ke Æ™oÆ™arin shigowa É—akin nasa, da mamaki ya ce, “Ahmad kana lafiya kuwa? Ina zaka haka?”.


    “Yaya babu lafiya, na aikata babban kuskure wlhy.”


   “Kai miye haka wai, nutsu mana”.


 Coach ya sake faÉ—a yana riÆ™o Ahmad da ke Æ™oÆ™arin turesa ya fita. 


     “Yaya dan ALLAH kayi haÆ™uri idan na dawo zan maka bayani. Aliyu ne ya kirani...”


  “Kai bana son shashancin ka nutsu kamun bayani mana”.


    Rasa mi Ahmad zaice yayi, sai kawai cikin matuÆ™ar gundura ya ce, “Asibiti yaya. Asibiti zan kaisu, na tabbata koma minene yanada alaÆ™a da abinda na aikata wlhy. Dan girman ALLAH ka barni naje”.


      Hankalin Coach ya fara tashi shima, dan Ahmad yana magana ne kamar zai yi kuka. 


   “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ahmad Please ka faÉ—a min mike faruwa? Miya samu Aliyun ne? Mika aikata masa kuma?”.


      “Yaya nayi kuskure, abu na saka musu a fura, bana raba É—ayan biyu koma miya tada hankalin Mawashi nada alaÆ™a da abinda na aikata É—in. Yaya kamarfa kuka yakeyi da tabbatar min zai rasata. Yaya ka barni naje dan ALLAH”.


    Kai Coach ya dafe domin ya samu amsar abinda ya kawoshi sashen Æ™anin nasa dama. Dan dama matarsa ce ta bashi maganin da Ahmad É—in ya yarda É—azun batare da ya sani ba kuma an É“alla maganin, kasancewarta likita yasa hankalinta tashi fahimtar maganin datai kona minene. Taso danne zuciyarta ta binciki Ahmad É—in ita kaÉ—ai amma saita kasa haÆ™uri ta tunkari mijin nata da batun shine dalilin fitiwarsa zuwa inda Ahmad yake. Yanzu kuwa jin zantukan Ahmad É—in ya tabbatar masa su Aliyu ya bama maganin ke nan. Ba lokaci bane na dogon tunani, dan haka ya ciro wayarsa da ga aljihu yana faÉ—in, “Kaga bari Khadijah tazo kuje tare, yanzu dare yayi duk asibitin da zakuje zaku iya fuskantar matsalar ganin doctor.”


    Tuni Lulu ta sake fita a hayyacinta wa Smart, zuwa yanzu kam koda ya zuba mata ruwan ma batako motsa ba. Sai kawai ya dafe kansa dake wata irin masifar sara masa. Ya auna kiran Ammah sau shuri masaÆ™i zuciyarsa na gargaÉ—insa. Hakama Abba. A wannan halin ya tsinkayi horn É—in da yake Æ™yautata zaton na Ahmad ne. Zumbur ya miÆ™e ya fito, dan yasan dole sai ya buÉ—e masa gate ya shigo. Doguwar riga ya samo ya saka mata, dama shi tuni ya suturta nasa jikin. Yana buÉ—e gate É—in bai jira Æ™arasa shigowar Ahmad É—in ba ya juya cikin gidan da sassarfa. Fitowa aunty Khadijah tai tabi bayansa, yana Æ™oÆ™arin shigewa bedroom ta kirayi sunansa. Da sauri ya juyo dan shi idonsa ma yay rufewar da bai kula da ita ba, sannan ya manta ma ita likita ce har sai da tai masa bayani. A tare suka shiga É—akin, ta ajiye É—an akwatin dake hannunta ta haura gadon ta É—agota Lulu zuwa jikinta....


   Smart da gaba É—aya dauriyarsa ta gama Æ™arewa cikin sarÆ™ewar murya ya ce, “Aunty mun rasata ko?”.


     “A'a Aliyu da ranta. Dan zuciyarta na harbawa suma tai kawai. Amma miya firgitata haka? Dan irin wannan sumar mai nauyi mummunar firgici ko tsorata mai tsanani akan abinda mutum baya so ke kawota”.


    Kasa bata amsa yay dan tana cikin mutanen da a rayuwa yake matuÆ™ar ganin girma da jin kunya. Itama fahimtar hakan ya sata cewa, “Shike nan É—an bani waje mugani”. Babu musu ya fita, inda ya samu Ahmad a falo na faman kai kawo. Da sauri ya taresa da tambayar “Ya ake ciki?”. Zaune Smart ya kai cikin kujera dan ji yake jiri na É—ibarsa kamar zai zube a Æ™asa shima. Ya dafe kansa da duka hannayensa kamar bazai cema Ahmad É—in komai ba. Sai zuwa can ya furzar da zazzafan numfashi ya É—an kallesa ya girgiza kansa, dai-dai nan Aunty Khadijah ta leÆ™o ta sake kiransa. Ta shi yay cikin Æ™arfin hali ya nufi É—akin. Batare da aunty Khadijah ta kallesa ba tace, “Kaimin ita Bathroom ka sakata a ruwan dana haÉ—a, ka riketa da Æ™yau dan zata iya zabura”.


   Duk yanda tace masan hakan yayi, sai ko gashi Lulu tai wata gigitacciyar zabura lokacin da yake sakata a ruwan. Da Æ™yar ya iya rirriÆ™eta ajiyar zuciya mai nauyi na suÉ“uce masa yayinda wanin sashe na zuciyarsa ke matuÆ™ar jin tausayinta da jin haushin kansa mai tsananin gaske. Sai da ta shafe kusan minti biyu tana fisge-fisgen kafin ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai ambaton sunansa da kausasashiyar muryar ta data gama É—ashewa cikin roÆ™o da magiyar ya barta, karya aikata. Kalamaine data dinga roÆ™onsa da su a lokacin da ya gaza amsa mata dan yakai fagen da bazai iya fahimtarta ba a lokacin. Goshinsa ya haÉ—e da nata yana ambaton, “Kiyi haÆ™uri Mawaddat kiyi haÆ™u......”


    Bai kai Æ™arshen kalma ta Æ™arshen biyar É—in ba ta Æ™walla wani masifaffen Æ™ara da zabura........✍️

No comments