Ingarman Namiji 1-2
Page 1 & 2__ababban filin jirgin saman mlm aminu Kano fasin jojine ke saukowa daga jirgin kowanne jayeda jakkar
kasanya..daga gefe nahango wasu jibga jibgan sojojine tsaitsaye kowanne da bindigarsa Kamar masu
jiran yak'i.
Wani natashin saurayine kesaukowa cikin isa da tak'ama tafiya yakeyi cikin takon irinna k'ak'k'arfan
namuji farineshi tassss gashi kyakkyawa nagaban kwatance Dan karamun bakinsa yamotsa tareda
yamutsa kyakkyawar fuskarsa yace Ahmad kunkiyi magana da Abba kuwa ? Yafada cikin sweet voice
dinsa.. no shinake k'ok'arin Kira tin d'azu Amma baya tafiya bansan miye matsalar ba..jiyowanayi Dan
ganin Waye Wannan Ahmad d'in domin kodajin yadda yake fidda zance cikin kalama da nutsuwa abun
gwanin Sha,awa.
Masha Allah nafada alokacin Dana ganshi domin shima d'in kyakkyawa ne ba garya sedai shi Ahmad ba
fari bane Kuma baza,a kirashi bak'i ba fatarsa Kuma wani irin shek'i takeyi na ban mmki.
Takowa yayi har inda Wannan saurayin yake tareda dafa kafadarsa Yana fad'in yawwa Yama shiga tareda
Kara wayar akunne. Cikin sauri d'aya saurayin yakarbe wayar tareda fadar hello abbahhh yaja sunnan
cikin shauk'i dafarin cikin shakar iskar kasarsa ta haihuwa...d'aya bangaren Abba ya,amsa tareda fad'in
SADEEQ gamasu d'aukarkunan sunzo munyi magana da YAZEED kaji son.
Lunshe fararen idanuwansa yayi kana yace ok Abba tareda yanke wayar Yana mikawa Ahmad abarsa
kana yajuya yana fuskantar jirgin bega kowaba numfasawa yayi kamun yadube Ahmad yace miyasa be
fitoba? Kamun Ahmad yayi magana sukaga yasawo kafa d'aya awajen matakalar jirgin kamun yasauko
data biyu yafito gaba daya Yana tako cikin kuzari da izza.
Kallo duk suka bishi dashi kamun ya,Ida k'arasowa kawai suka rankaya zuwa inda sukaga dandazon sojoji
na dunfarosu motoci akalla sunkai 15 sukazo d'aukarsu Amma mota daya suka shiga suduka ukku
saurankuma sojojin suka shiga sukad'au hanya.
Seda suka d'au hanya kamun sadeeq yakallin wannan daya fito daga baya yace yoshe kakira Abba
YAZEED? D'agowa yayi yakalli sadeeq da mayatattun idanuwansa yawatsamai su kana yamayardasu ya
lumshe batareda yace komaiba.
Nikam ai dask'arewa nayi Ina kallan kyau zaharaninshi domun kuwa tsakanin SADEEQ, AHMAD, YAZEED
narasa wanne yafi wani kyau aji izza tak'ama hutu dakuma jarumta.
Asalinsu
Family d'aya ne gabaki d'ayansu yarane sa,annin juna Wanda bazasu wuce shekaru 28 ba zuwa 30 Kuma
akwai shakuwa me tarin yawa tsakaninsu
Iyayensu su hudu ne agun nasu iyayen ALH.ALI shene babba wato Abba Kuma shine mahaifin AHMAD
y'ay'ansa 4 ne akwai Sameer da Salman se auta fauza..se ALH.AMINU shike binsa Kuma shine mahaifin
YAZEED shine kawai d'ansa dagashi bekara haihuwaba..se ummyy itace kanwarsu Kuma itace mahai fiyar
SADEEQ itama yaranta 2 sadeeq da siyamah.. se auta ALH.ZAYYAN shiko yaranshi ukku duka Mata. Anty
khadi anty lele se sumayya
Sadeeq shine aka farahaifa a family yanada kwana 8 aduniya aka haifi YAZEED shiko yanada wata daya
aka haifi AHMAD dukansu suntaso cikin soyayyar iyayensu da kaunar junansu basasan abunda ze taba
wani daga cikinsu.
Ahmad mutinne me hakuri da nutsuwa idan kaga Ahmad na fada to d'aya daga cikin yan,uwansa aka
tab'a... sadeeq kuwa mutinne mesan Wasa da raha barkwanci da sauransu..Sabanin YAZEED da yakeda
zuciya da zafin Rai Kuma bayasan raini ko kad'an.
Dukansu miskilaine Amma Ahmad da yazeed sufi zama asalin miskilai musamman yazeed...ahakan
sukayi karatunsu harsuka Gama sa,annanne kowanne yazab'i karatun dayakeso Amma ganinn cewa
yazeed soja yakeso yasa dukansu suka karanci sojan tareda goyon bayan iyayensu inda sadeeq dakesan
yayi Dr seya fito a Dr cikin sojojin..
Cigaban lbr
Awani tabkeken gida suka tsaya aka bud'emusu Gert sukadanna hancin motarsu ciki gidan katone
nagaske pert 5 ne agidan 3 na iyayensu daya na samarin gidan daya Kuma na kakannisu.
Dukan mutanen gidan sunfito tarban yaran nasu cikin faren cikin suke cikin ahlinsu gabaki d'aya suka ran
Kaya zuwa shashen abba domin dukansu anan suka taso. Gun jajiya mama.
Bayan sun huta anyi gaishe2 suka tashi sukunufi pert dinsu..
Ashagon tela nahango wasu yammata tsaye su biyu se haya Niya ketashi ga,alama fadane akeyi ko
wani,abun ke faruwa awurin,.
Karasawa nayi Ina mmkin Wannan abun.
Karasawana yayi dededa wankawa wani saurayi nari da d'aya budurwar tayi jikinta ko,Ina rawa yakeyi
Kamar an jona Mata lartanki daya budurwar kuwa se rek'eta takeyi sukuma mutannan wurin nafadar
tayi Dede.
D'agowa tayi ta kwace hannunta daga rikonda d'ayar tayi mata.
Masha Allah watafarakallah bi ahasanil haliqeen
Hak'ik'a Wannan duk inda ake Neman kyakkyawa tazarta Nan
Kalon mutumin data Mara tayi cikin fushi da tsiwa tace kayi ganganci Kai hannuka jikina kasani bako
wacce mace bace marar tabiyya irinka wlh wlh wlh sekayi nadamar tabanin dakayi banza Dan
akuya...Tana Gama fadar hakan tafigi Jakarta tayi waje wadda suke tare nabiyeda ita Bata tsaya ko inaba
se office din Jami,an tsaro cikin kankanin lokaci tagama abunda zatayi segayad'ai Yan sandan sun biyosu
amotarsu
Shagon telannan suka dawo Babu Bata lokaci akayi gaba dashi tareda kulle shagonsa.
Sannan hankalin yarinyar yadawo jikinta tasauke wani k'ak'k'arfan ajiyar zuciya tana fadar nagama da
Wannan matsalar Kuma..harara Amina dasuke tare tawatsa Mata tareda cewa seki San,abunda Zaki
gayawa anty khadi wlh Dan baruwana domin kinsan abunda tace..Ido budurwar tazaro tareda murguda
baki tace.......
Hummm muje zuwa daiiiiiiiiiii
Autar ahairi✍✍
ALHERI WRITERS ASSO
A.W.A
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/
________________
INGARMAN NAMUJI
No comments