Furar Danko Book 02 Page 44


 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲





  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣




.......Smart ya samu zama da Daddy da ya shigo London a ranar da Lulu ke cika kwanaki biyar. A ranar sun buga wasa a cikin London ɗin ne, bayan sun tashi ne sukai zaman tattaunawa su uku harda Uncle Yousuf da ya shigo domin kallon wasan shima. Daddy ya damƙa masa camara, tare da tabbatar masa Sulaiman yana shiri na musamman a kansu. Dan a yanzu haka akwai wata yarinyar baturiya da ya gano an turota ta shiga jikin Smart ɗin. Shiyyasa ma yay azamar kawo masa matarsa kusa da shi saboda gudun kar'a samu akasi. Murmushi Smart yayi da firzar da iska. Kansa a ƙasa ya ce, “Karka damu Daddy in sha ALLAH babu abinda zai faru. Kafin na mallaki iyali nafi ƙarfin kaina ma balle yanzu da na tabbatar da har zuri'a na fara tarawa. In dai al'amarin Sulaiman ne yabar damunka, dan a yanzu haka a tafin hannunmu yake. Abinda nake buƙata a wajenka kawai yanzu bayan wannan camara ɗin shine list ɗin abokan huɗɗarsa. Sannan ka sa su Hassan subar Abuja su koma Kano gabanku. Dan Sulaiman ya fara kai musu hari ta hanyar aboki, a yanzu haka ana gab da jan ra'ayinsu da wani kasuwancin da nake ƙyautata zaton irin shigo-shigon da akai maka ne”.

      Sosai hankalin Uncle Yousuf da Daddy ya tashi, dan sam Daddy hankalinsa bai kai wajenba saboda wani babban business da ya dauki hankalinsa kwana biyun nan. Smart kuma bai sanarma Uncle Yousuf ba dan yakan ɓoye wasu abubuwan gudun tada musu hankali. Muryar Daddy har rawa take wajen faɗin, “Aliyu yaya akai kasan wannan kai da kake anan?”.

    Murmushi Smart yay masa, cikin shafa kai ya ce, “Daddy koyarwarka ce ai. A yanzu idanuna a buɗe suke akan duk wani motsin su Sulaiman da tawagarsa. Sannan Usman ya sake zame min cctv camara. Dan yanzu haka yana Nigeria yin wani aiki da ya shafi hakan ma. Sannan Uncle Yousuf shine jagoran tafiyar,..”

     Da sauri Daddy ya dubi Uncle Yousuf. Murmushi yay masa ya kauda kansa shima. Smart yay dariya shima da cigaba da cewa, “Mu yanzu fatanmu Daddy kaje ka kwanta abinka ka huta. Karka damu da duk wani ƙulle-ƙullensu dan biye muke da su. Yanzu haka a daren jiya sunyi zama kanka harma da Abba. Sannan akwai kayansu dake hanyar shiga Nigeria. Kayane masu nauyin gaske da suka haɗa kusan kaso bibbiyu na dukiyarsu domin kawosu, dan mugayen kayan shaye-shayen ne kawai a cikinsu da in har suka samu shigar da su zasu samu maƙudan kuɗaɗe. Target ɗin mu yanzu muna zargin Sulaiman nada Company na sarrafa magunguna a ɓoye, sai dai bamu san a ina Companyn yake ba, shine muke bibiya domin mu tabbatar...”

        Ji Daddy yay kamar ya saki kuka, hannayen Smart da Uncle Yousuf ya kamo a cikin nashi, sai ma ya rasa mizaice da su. Sai ga hawaye kawai na gudu a fuskarsa. Da ga Uncle Yousuf har Smart rikicewa sukayi. A take suka shiga jera masa tambayoyi. Sai ya sakar musu murmushi yana goge ƙwallar tasa da faɗin, “Kunga bafa wani abu bane. ALLAH yay muku albarka. Ban taɓa tunanin zanga irin wannan ranar ba a gareni. Domin na ɓata tsahon shekarun girmana a tunanin yanda zan ɓulloma wannan al'amarin ne. A duk sanda nayi hangen sako su Hussain a ciki sai zuciyata ta ƙi aminta da hakan, saboda su sunada rauni. Sannan har yanzu suna a kan dokin ƙuruciya ne ba komai suke kallo a mai muhimmanci ba. Aliyu kai ɗan halak ne, nagodama ALLAH da yasa ka zamo mijin Mawaddat, na kuma godema ɗan uwana da yay wannan haɗin alkairi. ALLAH yay muku albarka. Ya kare rayuwarku da ta ahalinmu gaba ɗaya. ALLAH ya ƙara ɗaukaka ku, ku zama abin alfahari da babu irinsu a wannan zamanin. ALLAH ya albarkaci rayuwar Aliyu ƙarami da takwarana Isma'il (Ra'is) da Kamaluddeen, yasa suji ƙanku fiye da yanda kuka jiƙanmu”.

        Cikin rauni Smart da Uncle Yousuf ke amsawa da Amin. Smart na ƙara jin ƙaunar surukin nasa na ratsashi. Ga Uncle Yousuf Daddy ya juya. A hankali ya furta, “Nasha gaya maka Yousuf kaine babana a wannan matakin, narasa baba ne kawai a suna, amma ga babana a kusa dani.....”

     Cikin katseshi Uncle Yousuf ya ƙyalƙyale da dariya. Sai kuma ya rungumesa da faɗin, “Oh oh Yaya ni Wlhy kunya kake sakani, ni dai ba sai kace komai ba. Karka manta fa kaine na tashi nakema kallo a matsayin mahaifi kai da aunty Khareema. Kun raineni tun bansan kaina ba. Kun gatantani tun baku san minene daɗin ƴaƴa ba. Wlhy raina fansa ne a wajen kare ku daga duk wani maƙiyi da zaice kune abin harinsa. Ni dai fatana ka cigaba da kwantar min da hankalinka kawai da mana addu'a. Sannan ka janye mana ra'ayin su ƴan biyun kamar yanda Aliyu yace shine kawai aikinka.”

     Kasa cewa komai Daddy yayi, Smart dake saurarensu yana murmushi ya ɗan fesar da numfashi yana ɗan jujjuya camara ɗin. “Inaga a wannan gaɓar ya kamata Mawaddat ta fara aikinta. Dan haka zan duba abubuwan cikin camara ɗin nan tare da ita. Sai dai ina jin tsoron al'amarin ta dan bata da haƙurin kawaici ma abu, zata iya buɗe mana aiki da wuri wlhy”.

       Yanda ya ƙare maganar cikin marairaicewa ya saka Daddy da Uncle Yousuf kwashewa da dariya. Dan kuwa suko suka san wacece Mawaddat. Daddy yace, “Aliyu kamar kasan abinda nake tunani kenan ALLAH. Dan Mawaddat yanda kasan zawayi haka take. Ballema ta ƙullaci Sulaiman ɗin a yanzu, dan bakaga yanda taima Dada bane ba ma fa. Abinda kawai zamuyi shine da zarar kun gama gani sai mu samu lokaci mu zauna da ita mu duka kafin na wuce. Sauƙin ma ga babanta da ya san matakan bida ita yanda ya kamata sai kaga tayi abinda ake so”

      Murmushi kawai Uncle Yousuf ya keyi shi dai. Yace “Ku gama gulmarta duk sai na faɗa mata ai, dama kun mata wayo kun kawota nan. kai kaine za'a hana tuwo”... Yau maganar yana nuna Smart.

      Dariya Smart da Daddy keyi, Daddy yace, “Sauƙin abinma kaine gaba-gaba wajen ƙullawar dan nayi recording.”

    Smart ya kasa daina dariyar waɗan nan mutane. Komai nasu a sauƙaƙe cike da ƙauna da soyayyar juna. Suna ƙara masa ƙaimi akan ƙaunar ƴan uwansa shima.....


      _______★


     A ɓangaren Lulu tun fitar Smart itama ta fice a gidan. Asibiti ta nufa saboda maganar Smart dake cimata rai akan shi baya saɓa saiti. Haka kawai take jin tsoro a ranta, ita yanzu ta samu ciki kuma ai taga bonu. Yaushe ma yaronta yay ƙwarin hakan. Bawai bata son yara ba, amma dai tafi son ko zata sake haihuwa sai AA ya kai irin 5years haka. Yanzu kam tana ina zata fara haɗama kanta cakwakiyar nan, ga business ga rainon AA, ga fitinar ubansa, ga rainon ciki da hidimar ƙungiya dana aikinta. Ta samu ganin likita, babu wani kwana-kwana tace planning zatayi, amma su fara tabbatar da babu wani abu a jikinta, duk da dai a ganinta haɗuwa uku bai zama lallai a samu wani abu ba, to amma idan tai la'akari da farkon haɗuwar aka samu cikin AA sai hankalinta ya sake tashi taji ta kasa yarda da kanta. Doctor dai ta mata dukkan abinda ya dace sannan ta bata magani, acewarta a iya bincikensu mahaifarta fresh take babu komai. Amma ga magani tasha koda ma an samu akasi marar zata sake wankuwa fass. Daga haka suka saka mata abu a jiki ta dawo gida tana jin hankalinta a kwance. Ta iske har lokacin Smart bai dawo gidan ba. Dan haka ta ƙirƙiri aiki dan zama waje ɗaya ya isheta. Tsaff ta gyara gidan tare da musu girkin Nigeria yau. Tana kammalawa tai wanka, kayanta da ya rage ɗaya tak ta saka ta dawo falo ta zauna dan AA tunda suka dawo barci yake abinsa. Ta shagala a kallo ya shigo gidan da sallama hannunsa ɗauke da kaya. Bata motsa da ga inda take ba ta dai zuba masa ido, shiko nashi idanun na kallon gidan ne da yanda aka gyara shi, aka canja zaman abubuwa da yawa. Gyaran mace dabanne. Ya ayyana a zuciyarsa yana ajiye kayan hannunsa a hankali. Kusa da ita ya kai zaune cikin yanayin gajiya ya ke faɗin, “Madam ya gidan?”.

        Baki ta tura da faɗin, “Ni ALLAH idan baka daina cemin Madam ɗin nan ba zamuyi faɗa ko kaima na saka maka suna. Sai kace wata tsohuwa?”.

     “Oh da yarinya kike ɗaukar kanki, ai kin tsufa tunda gaki da AA. Nan da shekara ashirin zaki ga anzo fara miki gaisuwar uwar miji”.

         Dariya ta ƙyalƙyale da shi, ta ce, “Kai kuma Baban miji ko”.

     Murmushi yayi yana ɗan girgiza kansa. Sai kuma ya lunshe ido ya sake buɗewa a kanta. “Ina boss ɗin gidanne naji shiru?”.

        “Barci yake, shiyyasa nake hutawa ta ai.”

    “Ai yanzu ga baban shi ya dawo hutu ya ƙare”. Yay maganar yana kissing kuncinta da kwantar da kansa a kafaɗarta. A hankali ta sauke numfashi da lumshe idanunta itama. Dan zuwa yanzu duk yanda taso cigaba da riƙe kanta salonsa na barazanar tonata ne. Ƙarfin hali ne kawai da taurin kai irin nata. A hankali ta ce, “Yaya wasan?”.

        “Alhamdullah bakin ƙi zuwa kallo ba”.

      “To ni Wlhy ban iya kallon ƙwallo bane”.

   “Sai ki fara koyo ai”.

“Zan ƙoƙarta in shan ALLAH kodan kai. Ni yanzu ma maganar da nake son maka shine jibi fa ya kamata mu koma”.

         Batare da ya buɗe idonsa da ga rufen da suke ba ya ce, “Ina kenan?”.

     A shagwaɓe ta ce, “Nigeria mana”.

“Uhhyim yin me?”.

Idanu ta zuba masa da mamaki, “Ya zakace yin me bayan kasan ayyuka na baro na taho nan, kuma ni da shirin sati ɗaya na taho ko kwana goma. Wlhy inada abubuwa masu yawa acan”.

       Kaɗan ya buɗe idanunsa yana kallonta, tsahon mintina kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya firzar da numfashi. Cikin deep voice ɗin nan nashi da babu wasa a cikin fitar sauti ta ya ce, “Mawaddat! Ke yanzu idan ance miki ki ƙara tafiya kibar mijinki sai ki tafi? Kiyi lissafi shekarar aurenmu ɗaya da wattani takwas kenan fa. Amma bamu taɓa zaman cikakken wata guda ba har yanzu. Idan ke baƙya jin damuwa da hakan ni gaskiya ina ji. Sannan haƙurina ya ƙare ina buƙatarku a kusa dani yanzu. Shekarunmu tafiya suke bakwai komawa baya ba, ko sai ƙarfina ya ƙare sannan zaki fiskanceni a gaɓar da bazan iya komai a gareki ba. Na waiga ma na ganku a kusa da ni farin ciki nake ji. A yanda nai wasa a fili yau kowa yasan ina cikin farin ciki mara misali, aure ibada ne fa bawai son zuciya ba ko ra'ayin kanka a yanda kaso tafiyar da shi. Dan haka maganar komawa na soke shi, ba yau ba, ba gobe ba babu ma rana kawai at all. Dan haka karma ki sake mun maganar data shafi hakan ranmu zai ɓaci ne kawai”. Ya miƙe fuska a tsuke ya bar falon zuwa bedroom........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments