Ingarman Namiji 17-18
Page 17 & 18
____zekunnah kenan wayarshi tafara rurin neman d'auki d'auka yayi tareda Kara wayar akunne
batareda yace komaiba..acan bangaren sulaiman kuma jin and'aga wayar yasashi fara magana domin
yasan bazeyi maganarba tin yayi shiru.."big man kanajina kuntaso kuwa?"No miyafaru ne? Yatambaya
cikin daddan vocie dinshi.."wlh yanzu GR yakirani yakecewa yakiraka baka d'agaba Kuma yawar Ahmad
baya tafiya Wai muyi sauri muzo yau zamushiga aikin domin matsalar takaru daga yadda mukasanta Dan
Allah kuyi sauri muwuce domin kukad'ai nakejira please.."ok badamuwa gamunan zuwa yafad'a tareda
katse wayar yamayarda computer shi wurinta kana yak'arasa shiryawa yafita.
Sulaiman abukinsune tin a school shida ma,aruf da yaseer Amma su bagarinsu d'ayaba suma zasu
bayyana idan lokaci yayi bayansuma akwai wasu mutanen dasu,nansu ze,iya bayyana agaba inafatar
kungane
Aperlo yasamu su Ahmad najiranshi suka rankaya suka fita zuwa pert d'in iyayensu daga big mom har
anty amarya addu,a sukayi masu sosai kana suka tifa zuwa pert d'in kakarsu alhajiya Nene ikon Allah
kenan.
Koda sukaje Nene nahakimce aperlo me,aikin big mom namata tausa..d'agowa tayi tana K'are musu
kallo domin tafe suke apelon cikin takon isa da tak'ama tafiya sukeyi irinta gwarazan maza cikin kuzari da
haiba daganinsu kaga cikakken mazaje masu jini ajika.
Zama sukayi dukkansu akusanta yayinda sadeeq yad'ora kanshi acinyarta suma suka zuba Mata Ido
bawanda yace komai..baki Nene tatab'e kana taguntsura goronta takaibaki kana tace "ohhhhh nidije na
naga abunda keshan jininjikina yanzu ku Dan Allah Dan annabi Dan kuga su wad'ancan sha,shashun
iyayen naku sun zubamuku ido shine kukamik'e Kuma azaune sekace bamazan kirkiba. tak'arasa zancen
tana kallan sadeeq daya d'ago shima Yana kallanta cikin alamar tambaya.. Ahmad ne yayi k'arfin halin
cewa"kamarya bamazan kirkiba Nene ?
"Ahhhabb yoto Ina mazan kirki anan kowanneku ze iya nome gona 10 alokaci d'aya Kuma yayi Mata
kyakkyawan banruwa tayadda za,asamu yabanya me kyau..Amma kunkasa kozancen auren ma bakwayi
dakuda iyayen naku bansan miye nufikuba koso kukeyi Sena mutu ohooo.
Shuru sukayi Mata bawanda yace komai domin duk basugano inda zancenta yanufaba se yanzu.."kunyi
shiru kunk'yaleni sekace Ina magana da kurame.."No Nene bafahaka bane zamuyi idan lokaci yayi Amma
kina mana zencen aure tinyanzu dukama nawa muke cewar Ahmad yak'arasa zancen yanadan yamutsa
fuska..
"Nono Kuma nonon uwarka kajimun d'anbanzan yaro daga maganar aure sekakawomin zancen wani
nono kanasan nonon ne kak'i kayi aure kasha harka yau naji bakantaccen yaro tafad'a tareda
dumgurewa Ahmad goshi.
Ido yazeed yazaro Jin yadda Nene tasauyawa Ahmad zance lokaci d'aya tareda saken murmushi gefen
baki Wanda yak'arawa kyakkyawar fuskarsa kyau da kwar jini..shidai Ahmad baki kawai yasaki Yana
kallan ikon Allah yakasa cewa komai yayinda sadeeq ketintsirewa da dariyar shak'iyyanci..kallanta
tamayar ga yazeed kana tace"yau aidole kamun dariya Amma ai tind'azu nake magana bakace komaiba
kaini wlh ma inatantamar lpyr ku dukanku domin indai lpy qalau kuke to doline kubuk'aci mace dominni
wlh Allah kab azuri,ata ba raggon maza Kuma ban haufi lusarin damace zata bawa tsoroba seku Amma
nasan mizanyi akai doline nad'au k'wk'kwaran mataki akanku wlh dagaku har iyayen naku.. tafad'a tana
hura hanci tareda ture dankwalin kanta gaba duka kwakkawar sumar kanta tabayya Takoma fara sool.
Murmushi kawai sukayi atare kana sukamik'e tareda gaya Mata zasu koma wurin aiki..Aiko tak'ara
hayyak'o musu damasifa tana fad'ar nankawai sukafi kauri sudai basuce komaiba abinka da miskilai seda
tagaji Dan kanta kana tamusu addu,a dafatan alkhairi kana sukafice..sunafita sukatarar yaransu duk
sunkaraso sunajiransu motoci suka shiga tareda barin gidan Basu zarce ko,inaba se gidansu sulaiman
tinkamun suk'arasa sukamai waya shiyasa yafito suna k'arasawa yashiga sukawuce se filin jirgi...karfe
9:30am Dede jirginsu yatashi se birnin tarayya Abuja..
Yayinda k'arfe Tara Dede akasallami sumayya daga asibiti sukayo gida bayan ansha famada,ita akan
bazataje gidaba gidan anty lele zata koma anyi,anyi Tak'i yadda seda taji hajiya mama nawayada big
mom tana gayamata su Ahmad suntafi kana tayadda zata koma gida murmushi kawai Abba yayi dominsu
duk atunaninsu muta,nentane basusan ta,asar datayiba.
Unguwar Gama B Kano
SAURAT ce zaune itada Mami mahaifiyata kenan.."Wai SAURAT miyasa kikesaka Wannan kayan bana
hanakiba eye? "Baki taturo gaba tareda duban kayan jikinta rigace iyakarta gyiwwarta Kuma batada
wadataccen hannu kana saga2 take har underway d'inta anaganin kwancinsu."nifa Allah zafi nakeji
Mami banasan Wannan manyan kayan Allah.."tofa keyanzu kokunya bakyaji dalibanki suzo susameki
ahaka idan sunganki cikin zumbulelen hijab se arantse da Allah wata kamilace ke..baki taturo tareda
b'ata fuska cikin shagwaba take fadar "haba Mami yanzuni ba kamila baceba? "Ehhh lallai SAURAT
kekamilace Amma Bata fanni suturta jikiba Zakitashi kinemi suturar kurki kisaka kosena makeki..tashi
tayi tana k'uk'unai tareda bubuga kafafuwanta ak'asa duk ilahirin jikinta yad'auki girgiza..Ido nazaro
kamun nasake murzasu Ina Kare Mata kallo lallai SAURAT takai duk inda cikakkiyar mace kekai domin
tsakanin SAURAT SUMAYYA dakuma BUDURWAR jeji narasa wacce tafi wata diri kyau dakuma.....nayi
shiruahakan tawuce bedroom d'inta tareda rufe k'ofar Kai kawai Mami tagirgiza tareda rokon Allah
yakare Mata tillon Yar tata.
Abuja
Tsaitsaye suke cikin wani katon office gadukkan alamu nanne office d'in GR kowanne ak'ame Yana
saura,rar abunda megidan Nadu kefad'a
"kusani Wannan shine damar damuka samu akansu domin duk sakonda suke turo Mana alokaci d'aya da
mabanbanta nomber da wurare daban2 Dan su hargitsa Muna lissafine karmu gano shirinsu sund'auka
muma marasa tinanine kamarsu shiyasa mukayi k'wak'waran bincike akan komai nasu Kuma insha Allah
yanzu munyi Shirin tukararsu akowanne yayi bagudu bajadaba kusani domin sugano yanlek'en asirinmu
yanzu hakan farautarsu sukeyi Kuma Kunga bakayan aiki ataredasu inafatar kungane bayanina.?
"yers Sr suka fad'a gabad'aya.."Masha Allah tinda kunfahinta yanzu Kai sadeeq da sulaiman zaku
jagoranci shiga jejin yobe state yazeed da Ahmad sujagoranci jejin barno state Yusuf da manir zaku
yagoranci jejin Zanfara state yanzu kowa yad'ibi yaransa ku d'au hanya Allah yakareku.."ameen y Allah
suka ansa atare..kana suka fice kowanne da,abunda yakesak'awa aransa suna masujin zafin rabasun
da,akayi wurin tafiyar..ahakan kowa yad'ibi yaransa suna masuyiwa juna fatan nasara sukarabu inda
sadeeq da sulaiman su d'au hanyar yobe yayinda yazeed da Ahmad suka d'au hanyar barno...
Asauka lpy matafiya.
Gaskiya inbaga comment me ratsa zuciya ba bazak'uga update ba har week d'innan yak'are
Free page yakusa k'arewa idan kinshirya karatun INGARMAN NAMUJI to kihanzarta sayan naki tahanyar
datadace #500 kachal idan kintashi siya Zaki iya yimun magana tawannan nomber 07037092176
Autar alheri✍
ALHERI WRITERS ASSO
A.W.A
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/
_______________
INGARMAN NAMIJI
No comments