Ingarman Namiji 15-16
Page 15 & 16
__Akayi wani mugun ihu da gurnani me firgitarwa cikin tashin hankali suka Ida kutsakai ciki Dan ganin
mekefaruwa.. sumayya ce atsaye tsakiyar d'akin tad'aga gadon d'akin sama da hannu d'aya tana gurnani
idanuwanta duka sunjuye tanashirin dokawa anty lele shi aka..cinkin matsanancin sauri yazeed yayi
cikinta tareda rik'e hannayenta duka suka D'ora zagayen d'akin dagadon ahannusu..cikin firgici hajiya
mama kefad'ar nashi ukku ni hajara mizangani haka yazeed saketa karta illataka saketa nace..ah,ah
mama ba,abunda zefaru kufice daganan inasan sauke bed dinne.."ah,ah fa yazeed.."no mama kufitanace
yafad'a dad'an d'aga murya sabida ganin tanasan jefama wani acikinsu cikin hanzari suka fice hajiya
mama naciro wayarta tadannawa abba kira itako anty lele duk tarud'e tamarasa mizatayi itama wayar
taciro takira anty amarya tagaya Mata abunda kefaruwa..atake kuwa cikin tashin hankali anty amarya
taje sashen big mom tagaya Mata Dan ita bazatajeba sabida kawaici..itama big mom hankalinta yatashi
sosai batako tsaya Kiran abbu ba tafito tana fitowa taga Salman da Ahmad gayamusu tayi tareda cewa
sukaita hospital din hakako akayi suka nufi asibitin cikin gaggawa.
Bayan fitarsu hajiya mama kuwa danbene yakaure tsakanin yazeed da sumayya Dak'yar yasamu Kai
bakinshi kunneta yafara reramata karatun Al,qur,ani cikin suratul baqarah cikin dakiya da
jarumta..gurnanin datakeyine yak'aru tareda karak'aimi wurin San lahantashi..shiko yarik'e hannayenta
da,iya k'arfinshi..cikin Jin zafin karatun dayakeyi akejijjigasu taredasan kwacewa Amma Ina abun yacitira
hakan yasa sukayi jifada gadon suka jiyo gareshi..shikuwa yazeed jiyowarda tayi yabashi damar mird'e
hannuwan tareda jefata akan gadon.
Aiko yazumbur tayi zata Mike yayi saurin danneta tareda sake Kai bakinshi kunneta yacigaba da karatun
dayajeye..
Acan waje kuwa tuni su big mom suka k'araso anan suka Sami Abba da abbe Amma dady bezoba suna
zuwa hajiya mama tacewa Ahmad "Kai shiga ka temakawa Dan uwanka kada su illatashi..cikin sauri
yanufin d'akin yad'ora hannusa kenan yaji ance dakata Ahmad.
Dakatawa yayi sabidan Jin muryar data dakatardashi tareda duban memaganar ummy yagani tafe
mahaifiyar sadeeq itada siyamah...k'arasowa tayi tana fadar "barsu dashi karkashiga..kamarya
karyashiga zainab? Kinajifa abunda kefaruwa inta jimasa ciwofa tinda ba karfinta bane.."to hajiya mama
inya temakeshi yanzu gabafa Waze temakeshi ai gara yasaba tin yanzu..shiru hajiya mama tayi Bata sake
maganaba yayinda Ahmad Kebin anty tasu dakallan mmki.
Ad'akin kuwa
Mutanen na sumayya ganin yazeed naneman k'onasu yasa suka fara magana cikin wani sauti me
firgitarwa maraddad'in sauraro "kabarmu karka konamu kasani idan kak'onamu bazamu taba barinkaba
daga Kai har ahlinka sumayya tawace ni kad'ai duk lokacin daga sake Bari taga wani abun asashen jikinka
harya burgeta to wlh Niko senaga bayanka nine kawai Wanda zatakalla yabirgeta nine kawai nata itad'in
tawace nikadaiiiiii.. yak'arasa zancen cikin hargagi
Shikuwa yazeed ko,ajikinshi katan kawai yakeyi bebi takan zantukan dasukeyiba ganin k'onasu zeyi
bilhak'k'i yasu fita bashiri sunafar karyasake Bari yarab'e sumayya tareda jadda da Masa zasu
dawo..gabaki d'aya sumayya zubewa tayi ajikinshi dama akwance suke agilme tamatseshi ajikin bango
yanzuko duka jikinta yasake senumfashi take saukewa ahankali alamar bacci takeyi..shiko kallanta kawai
yakeyi ana tinanin ai doline tasamu gayyar fasinjoji kodan Wannan Rashin Jin nata sun dad'e ahakan
sumayya mak'alle ajikinshi shinfed'eta yayi gefe kana yatashi yagyara jikinshi kana yafita..atare duka
suka k'araso suna tambarshi Yaya jikin nata musamman hajiya mama datake cewa "yayadai son hope dai
ba,abunda sukama ko? Tafad'a tanashafa gefen fuskarshi Allah yasani tana mugun San yazeed dudda
ba,ita ta haifeshiba.. murmushi yayimata kana yakwantarda kasan akan kafad'arta bayan tazauna bakin
gadon da sumayya kekwamce Yana fadar"am okay my mama ba,abunda yasameni tareda sumbatar
hannuta..itadai big mom murmushi kawai tayi domin tana ganin zallar sonda hajiya mama kewa yazeed
ak'wayar idanta Wanda take tinanin ko itadata haifeshi iya son dazata Masa kenan.
"Naji kamar suna magana minene suke fad'a son? Cewar abba.."no bakomai Abba shirmensune
kawai.."to allah yabata lpy yace. suka amsada ameen y Allah..kuzo muje gida domin Dr yace baze
sallameta yauba se gobe ke hajara kizauna da,ita tareda yazeed kaiko Ahmad ku,ajiye Maryam gidanta
Allah yabamu alkhairi..."Abbah gobe jirginmu zetashi fa karfe 9:00am..sadeeq yafad'a yanakallan
abba..to ai bawani abun seyakoma gida da,assuba sabida Wannan matsalar bazeyu hajara tazauna da,ita
ita kad'aiba..seku shirya Masa kayansa idan kunkoma kamun yazo..too sukace dukansu tareda yin
abunda yace.
Gidansu sulaiman
Dareyayi sudai Dan yanzu karfe 2:00am Marwan ne tsaye yana sallah bayan ya idar yadad'e zaune Yana
addu,a tareda kokawa Allah damuwarsu yad'au tsawon lokaci yanayi kamun ya kwanta.
Dakin shatu kuwa kwance suke itada baba lado cikin bacci baba lado yarik'a jiyo kukanta tashi yayi Yana
dubata zaune yaganta akan sallaya tad'aga hannayenta duka biyu tana addu,a tana kuka..k'arasowa yayi
kusanta tareda tallabota jikinshi Yana shafa bayanta alamar rarrashi dauriya irinta baba lado yau shima
seda yayi k'walla Amma yayi sauri sharewa kada matarsa taga rauninshi..ahakan yalallab'ata sukaje suka
kwanta tareda yimata nasiha meratsa zuciya akan d'aukar kaddara me kyau ko akasinta tareda karfafa
Mata gyiwwa akan muradinsu.
Washe gari
Lpy qalau suka kwanada sumayya ba,abunda yafaru Dan bacci matakeyi har yanzu bata farkaba.. yazeed
kuwa tin asuba Ahmad yazo yad'aukeshi suka tafi gida tareda yiwa hajiya mama bankwana..addu,a tayi
musu sosai dafatan nasara akan abunda suka sakama gaba..sunji dad'in addu,ar tata sosai kana sukayi
Mata sallamah suka tafi..suna fita masallaci suka nufa bayan sunyi sallah suka shiga gidan kowanne
yashiga shiryawa Dan sufita da wuri gaya sulaiman yace subiya sad'aukeshi Dan direban gidansu
bayanan Marwan Kuma zeje school tin 7 balle yayiwa baba lado magana yakaishi..zaune yake bayan
yagama shirinshi tsab Kaya kawai zesaka seya tuna Wannan zuwan dasukayi beduba abunda yafaruba
bayan sunyi waccan tafiyar atake yajawo computer shi mehadeda cc vt ze.....
Tofa yazeed nidai nayinan
Free page yakusa k'arewa befi page 3 ba yakare idan kinshirya karatun INGARMAN NAMIJI to
kiyihanzarta sayan naki tahanyar datadace #500 ne kachal idan kintashi siya Zaki iya yimun magana
tawannan nomber 07037092176 inkinsan basiya zakiyiba karki batawa kanki lokacin nemana kokice
namuki ragi ko akasin hakan domin bazanyiba karkiyi kice namiki wulakanci bana wulakanta kowa Amma
banasan reni maganin Bari Kar afara..
KARKIBARI ABAKI LABARI akwai chakwa kiya agaba
Autar alheri✍✍
ALHERI WRITERS ASSO
A.W.A
https://www.facebook.com/100186388252056/posts/
________________
INGARMAN NAMIJI
No comments