Soldiers Family 21-22
Page 21&22
__"jalaludeen da Al,Hassan agaba se abbe da mama
abaya.. perlon cike yake da ahalin Alhaji shuraim suna meeting saka makon auren
da aka d'aurawa samarin gidan ba bu shiri... Alhaji Imran ne ya d'ago yana amsa
sallamar da sukayi aiko yayi Ido 4 da abbe arazane ya mik'e yana fad'ar
Habeeb...hakan yasa gabaki d'aya mutanen dake perlon suka d'ago suna kallan
k'ofar dan gaskata abunda sukaji abbansu na fad'a.
Aiko dai shid'inne ba wani ba kamun suyi wani motsi tuni
Alhusain da Suhaif sunkai bakin k'ofar suna k'ara ware idonsu Dan sunkasa
gasgata abunda idonsu kegani...ganin sunyi tsaye sunka cewa komai yasa
Jalaludeen cewa abbe nefa dagaske suhaif bawaniba aikamun yarufe Baki Suhaif ya
rungumeshi yana fad'ar, "abbe dagaske mafarki najeyi ko gaskiya?"
Yaya jalal "abbe wlh abbe ne abbe ne Husain zokaga..."cikin sauri
Husain ma ya rungumeshi tare da fashewa da marayan kuka yana k'ara shigewa
jikin abbe d'in hakan yanad'asu duka yarunguma Yana share k'walla..kamun
yasakesu Yana nufar Yan uwanshi da suka
zo gareshi cikin farin cikin sake ganinshi araye suka shiga rungumarshi
dukkansu d'aya bayan d'aya suna hamdala ga ubangiji talikai...sunjima ahakan
kamun Alhaji Jameel ya kama hannunshi ya kaishi har inda habibbty kezaune tana
sharar k'walla.
Duk'awa yayi ahankali yace yace habibbty na tare da fad'awa
jikinta yakankameta sosai ajikinshi Yana sauke numfashi itama habibbty hakance
takasance agareta wani irin farin ciki takejin kanta aciki marar misaltuwa gata
ga hasken idaniyarta yadawo..sunjima ahakan kamun kowa yasamu wuri yazauna
anasake gaisawa.. Jalaludeen ne yakama hannun mama dake rakub'e gefe yazo ya
zaunar da ita kusan abbe Yana fad'ar abbe kaga su Abba kamanda y'arka ya fad'a
cikin tsokana... murmushi abbe yayi yaname kamo hannun mama ya rik'e Gam tare
da cewa, "ba,abunda zesa namanta y'ata Jalal ina sane da ita...se alokacin
kowa ya kula da Mama" Aiko Ido ya koma kanta musamman samarin gidan domin
wani Dan iskan kallo shareef da Najeeb ke jifanta dashi na tsantsar
barinkanci...agefe d'aya Kuma Fahad ma yakafeta da Ido ko kiftawa Babu
karshedai kasa hak'uri yayi yace Yaya jalal wacece wannan black Beuty d'in?
Hararasa yayi kamun yace k'anwata ce domin Yar abbe
ce...Masha Allah cewar habibbty kamun race Yar albarka zonan inganki kinji?
Bamusuko mama tamik'e dudda yanajin yadda idanun wayannan mayun keyawo
akanta..kusan habibbty tazauna taname sinnarda kanta ak'asa.
Kowa shiru yayi yanata kallon abbe se,a lokacin yakulada
Babu sauran yaransu Kuma Babu ammy kallon sulaiman yayi yace ""inasu
Yusuf da Alyasat Lateep ko suna London ne? "" Aa abbe sunan barana
kirasu" ya fad'a tare da barin perlon
"Sannunki y'ammata cewar shareef Yana kallon mama...
d'agowa tayi taga yadda yaketa wani lashe Baki Yana k'ib,k'ibta Ido Aiko
tazabga mishi wata uwar harara kamunta mayarda kanta k'asa batareda
ta,amsaba..Ido ya zaro yace fa🤔 dariya sukayi lokaci d'aya ganin yadda
tawani taderai...suhail yace gaskiya abbe wannan Yar taka akwai tsiwa batasan
gidan sojoji tashigo bane inda za,agyra
Mata zama...ah,ah fa bawanda zetab'amun y'a tinyanzu ma gara kusani...Zaid ne
ya balla Mata harara shima yanajan k'aramun tsaki dominsha yatsani
reni...ungunan Zaid dady yafad'a Yana Ware masa hannuwa dukkansu sukayi dariya
kamun wani yace wani abun Sega sulaiman da lateep sunshigo yusif na bayansu
warin ihu Lateep yayi Yana zaro Ido tare da fad'ar abbeee dak'arfin gaske hakan
yasa Alyasat daya tsaya waya shigowa perlon babushiri..shiko Yusuf mutuwar
tsaye yayi yamakasa cewa komai ganin dagaske abbenne gashi har Lateep yaje
wurinshi yasa shima yaja kafafunshi ya,Isa dukkansu rungume abbe suna kukan
farin ciki shiko se shafa bayansu yakeyi Yana murmushi.
Alyasat kuwa yakasa motsi tunda yashigo perlon kallan abbe
kawai yakeyi lus of control gawanu mugun bugawar zuciya dayakeji tinda
yadunfaro perlon....ganin yak'i shigowa Kuma yak'i komawa yasaka abbe mik'ewa
dakanshi yazo wurinshi tare da riƙoshi yace yaron ammy nine fa ko baki farin
cikin ganina ban..tinkamun yak'arasa Alyasat ya bashi wani kyakkyawan hug
meratsa zuciya matse abbe kawai yake ajikinshi Yana jujjuya Kai kamar ze
maidashi ciki kusan minti 5 ahakan seda yusif yace bro karka ballamana abbe fa
wannan matsa haka...seda yabawa kowa dariya kamun alyasat yad'an d'ago abbe
daga jikinshi yana hararar yusif kana yace abbee cikin wata raunanniyar
murya..na,am yaron ammy Kuna lpy?
Shiru yayi Yana kallan abbe Jin tambayar dayayi masa kamun
yasakeshi yanadanyi baya kad'an tareda kafe abbe da Ido cikin kallon tuhuma wa
mahaifin nashi kana yace abbe dama kana Raye kabarmu? Abbe aina kaje duk tsawon
shekarunnan? Abbe kasan awanne Hali ammy take? Abbe kasan wani abun mukeji
aranmu Idan muka bede ido bamu gankaba why abbe why? Sekuma ya dafe
zuciyarshi...cikin sauri abbe yak'arasa gareshi tareda rikoshi yace alyasat Ina
ammyn ku? Miyasameta? Minene yafaru bayan barina gida? Shiru alyasat yayi Yana
kallon mahaifin nashi kamun yarik'o hannunshi kawai suka fita daga pert d'in
ganin hakan yasa duk mutanen wurin suka mara musu baya Jalaludeen ne ya kama
hannun mama Yana fad'ar muje k'anwata ahakan suka fito suna boye dasu abaya har
pert d'in ammy bedroom d'inta yawuce
dashi har bakin bed d'inta inda take kwance kamar matacciya domin rayuwarce
kawai ajikinta..
Karb'e hannunshi yayi d'agana alyasat Yana tallabo baiwar
Allah kamun yace innalillahi wa innailaihhiraji un alyasat miyasamu ma,Isha?
Mike faruwa ne Wai ? Yafad'a dagarfi tared a fashewa da kuka me cinrai...
habibbty ce tad'afashi tana fad'ar kayi hak'uri habibullah daga ranarda aka
wayi gari baka d'aga wannan lokacin mukarika ganin chanin abubuwa awurin
ma,Isha sedai ba Wanda yakawo komai aranshi saboda atinanin mu damuwar
rashinkace sai dai Ashe abun ba hakan bane domin se gaba yakeyi bayan wata biyu
da tafiyarka ma,Isha Takoma azaune Bata iya komai ai anmata muskarta kawai zaka
kallan kagacewa ita me lafiya ce ahakan aka duk'ufa nema Mata magani ba asitin
da yarannan Basu kaitaba Amma abun yaci tura dak'arshe Kuma ciwon yak'ara
tsanan izuwa yadda kaganta ayanzu..tinda habibbty tafara magana wurin yayi tsit
ana saurararta ba,abunda ketashi adakin se kuka abbe Dana Al,Hassan gabaki
d'aya zuciyar kowa tayi rauni.
Acan waje kuwa jalaludeen ne kefamada mama akan tashigo cikin
gidan ammafa Abu yaci tura domin takafe kabb wuri d'aya Kuma yayi maganar
duniya takasa Koda dogon motsi...abunda Jalaludeen baisani ba miyagun aljanun
da suke part d'in ammy ne suka hanatashiga wanine daga ciki yarik'e ta domin
tabbas tashiga gidan za,asamu matsa babba akan aikinsu...shiko jalaludeen ganin
yayi da k'arya yayida gaskiya tashiga Taki se kawai yazaro wayarshi yakira
alhassan domin layinshine akai hakan kawai yaji baze iya d'ayawa yabartaba Don
yakira abbe garaya Kira wani agayawa abben.
Kamar Kuma yasan abunda kefaruwa domin wannan hatsabibin
aljanin dagawarshi kawai yake jira yad'auketa...bugan duniya yayi Alhassan be
d'auki wayaba se kawai yakira najeeb Yana d'agawa yace najeeb gayawa abbe fa
zaraah Tak'i shigowa.."okay kawai yace tareda juyawa yace abbe Yaya Jalal
yace Wai zaraah Tak'i shigowa...kowa dake wurin kallunshi yayi alyasat Kuma
seda zuciyarshi tabuga kamar zata balle tafito fili sabida kawai wannan sunan
da,akira atake yaji yatsani me sunan dudda besan kowacece ba Amma dajin yadda
zuciyarshi ke bugawa yasan Babu alkairi atareda ita..
Wacece zaraah? Zaid yafad'a azafefe domin yayi tinanin marar
kunyar yarinyar Nance dasukazo da,ita...shiko abbe ajiye ammy yayi tareda Kama
hanyar fita hakan yasa Yusuf Sulaiman Fahad Lateep Najeeb din duk sukabi
bayanshi Abba ma hakan dady kuwa habibbty yake rarrashi yayinda papu kezaune
perlo suka wuceshi domin tin farko beshiga bedroom d'in ammy ba.
Suko suna fitowa abbe yayi wurinda take tsaye k'ik'am kamar
andasata yace zaraan Abba miyasa bazaki shiga gidan abbankiba nanne gidana
zumushiga kinji yafad'a Yana kamo hannunta Amma yajishi k'age koma duk zancenda
yakeyi ko gizau batayiba..shiru yayi Yana kallon ikon Allah dudda yasan ba,ita
kad'ai takeba Amma yasan bazasu hanata shiga gidanshiba tinda da saninsu yazo
da ita hasalima da hannunsu suka bashi ita..shiko Jalaludeen kallonta kawai
yakeyi domin Beman artabon da bibibo yayi dasu ba a lokacin da suka harbi abbe.
Kowa dai awurin yayi shuru masujin haushi naji masu mmki
nayi Zaid da yafito daga baya shida alyasat dukkansu tsaki sukaja shidai gogan
zagawa kawai yayi yawuce yayi da Zaid yadaka mata tsawa Yana fad'ar keeeee Wai
wannan wanne iskancine abbe sa,ar wasarkine Yana magana kinyi banzadashi? Allah
Idan nazo wurin Sena ballaki kana nashigo dakai dak'arfi..."no bro karka
dajeta aibakuwa ce kawai kad'aukota dai kasan Abbi bazeji dad'i ba cewar Ameer
dashi isowarshi kenan...Aiko gadan gadan yanufeta Jalaludeen naganin hakan yace
Kai Zaid dakata banasan shirme...kafin yarube bakinshi kawai sukaga anyi samada
ita dak'arfi irin anjefarda abun d'innan...dukkansu Ido suka zaro suna bud'e
Baki madu kalima nayi masu salati nayi domin sunsanda tafad'o k'asa to seta
kakkarye wannan muguwar jifa kamar wadda aka jefar cikin tashin hankali abbe ke
fad'ar, "innalillahi wa innailaihhiraji un...."
*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500₦ kacal 👌 ga
duk me buk'atar complete kuma 700₦ ne Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar
wannan number 👉 07937092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉
08207819124
Autar Alheri ✍️
*S F*
No comments