Soldiers Family 19-20
Page 19&20
Free page yak'are daga wannan kiyi hanzari kinemi naki domin
karki Bari abaki lbr
__"amsawa sukayi duk suna kallanshi kana yasamu wuri
yazauna kusan mama yace""uwar gijiyata nayi bince akan sihirin sedai
kamar yadda anty halila tace doline sedake zamu karyashi nisawa yayi kamun
yasake cewa aikin Yana cikin ruwa acan akajefashi Kuma gudu yakeyi yadda wannan
sihirin ke gudu hakan abbanki zeyita yawo aduniya batareda sanin takamammen
inda zashiba ajiya nasaka antsayarda aikin inda zamu samu sauk'in kamashi
sedaifa bawanda ze iya fiddashi acikin ruwannan se bil adama sabida hakan Idan
kinshirya semuje.....kamun tayi magana jalaludeen yayi saurin cewa aa kabari Ni
muje ai wannan tayi k'arama kartasaka kanta ahad'ari...murmushi gimbiya halila
tayi kamun tace ba Wanda ze iya wannan se ita domin tana tattareda abunda bakadashi
sabida hakan kabari suje kawai kaide kayi musu fatan nasara...nisawa yayi kamun
yace shikenan Allah yabasu sa,a akan abunda zasuje nema... ameen y Allah duk
suka amsa kana mama tamik'e tana cewa bibibo suje mik'ewa shima yayi kana
maheerah ma tamik'e sukabar wurin seya rage daga gimbiya halila sesu mero
datawagar sojojinsu jalaludeen..!
Dubai
Alyasat nafita yawuce part d'in yusif aperlo yasameshi zaune
Yana aiki a computer d'inshi zama yayi kusadashi tareda jingina bayanshi jikin
kujerar batareda yace komaiba tinanin yake aranshi wannan wanne irin Bala,I ne
ace y'ay'a family d'aya Amma suna neman junansu Idan son muhibbat shareef keyi
baze auretaba itako dake fad'ar tana sanshi Ashe duka karyace Aiko zeyi
maganinsu....tinaninshi ne yakatse lokacinda yaji yusif nakiran sunanshi
yad'ago shima Yana dubanshi..."Miyake faruwa ne bro Naga kayi shiru se
tinani kakeyi? Dan yamutsa face d'inshi yayi kamun yace no bakomai kawai inasan
komawa London ne kamun mudawo bikinnan daza,ayi kaga daganan semu dawo aikinan
Baki d'aya ko?
Shiru yusif yayi nadan wani lokacin kana yace hakan zeyu
kuwa? "Eh mana kodama bazeyuba nibazan cigabada zama acanba domin gidannan
namu akwai matsaloli sosai gaskiya doline murik'a saka Ido gudun faruwar wani
mummunan abun...nisawa yusif yayi yace hakane bro to kodai kaga abunda kefaruwa
ne acikin stet d'innan?
Da mmki alyasat ke dubanshi kamun yace wani abunne yafaru?
"Humm zokaga yusif yafad'a Yana nuna masa abunda ke
cikin computer d'inshi...Ido alyasat yad'an bud'e kamun yadafe kanshi domin
abunda yagani yabashi mmki sosai dudda yaga wani shima Amma beyi tinanin abun
yake hakanba...ganin yayi shiru bece komaiba ne yasa yusif fad'ar yanzu minene
abunyi?
"Humm zamuyi maganinsu soon bro daga hakan bek'ara cewa
komaiba..ganin hakan yasa yusif fad'ar tashi muje mud'auko wani mlm danayi
magana dashi akan rashin lpyr ammy tind'azu yace mun suntaso nasan izuwa yanzu
jirginsu yakusa sauka daga saudia zezo...dobanshi kawai alyasat yatsayayi Yana
tinani aranshi inama ace dukan soldiers family kamar yusif suke sedai Kash
kowada kalar nashi ha layyar....seda yusif yarik'o hannunshi kana yamik'e suka
Kira lateep sukabar gidan..!
Ghana
Suna fita suka d'auke mama tareda shiga keta jejuka da ita
basuzarce ko inaba se wani k'aton teku Wanda mutin be Isa yace ga tsawon ruwan
ko fad'insu ba balle ayi zancen ganin karshensu seda sukakai Dede wani katon
dutse da ruwa kifita cikinshi suna gangarawa kana bibibo ya ajiye mama tareda
fad'awa cikin ruwan itako maheerah tana tsaye tareda ita duk wani aljani Idan
yazo wucewa yahangi mama seya kawo Mata Hari sedai daga zarar sun k'araso duba
d'aya suke Mata sukoma bashiri (komiyasa hakan🤔)
Yad'auki tsawon lokaci acikin ruwan kamun ya k'walawa
maheerah Kira Yana fad'ar yasamu ganin sihirin tashigo da Mama Aiko ko bakinshi
be rufeba tarik'e mama suka nutsa aciki can kasan ruwan wani katon ledane aka
nannad'e kamar ball ko tarewarda maheer yayiwa abun yakasa tsayi wuri d'aya
cikin k'araji yacewa Mahira tanunawa mama tad'auka domin masu tsaronshi gab
sukeda k'arasowa wurin...tana nunawa mama tasaka hannu biyu tareda bismillah
tad'auko Amma me tana rikonshi aka fara janta kamar igiyar ruwar zata tafida
ita ganin hakan yasa sukayi saurin fitowada ita ta gab'ar ruwan suna fitowa
maheer yace tadoka abun ak'asa Idan tayi hakan baze k'ara komawa cikin ruwaba
Kuma kowa ze iya k'arasa aikin
Hakako tayi domin dagewa tayida iya k'arfinta tadokashi
k'asa aitana dokashi itama ana wullata cikin ruwan hakan sukaga anjefata kamar
walk'iya kamun maheer yayi wani yunk'urin tuni maheerah tabi bayanta Amma se
tamaula ruwan keyida ita sunaneman hallakata dak'arfi gaske Mahira tasamu
nasarar cabkota kana tafitoda ita Amma tuni tasuma...seda suka B'ata lokaci
sosai wurin ganin sun ceci rayuwarta seda ta farfad'o dudda batadawo normal ba
kana suka shiga kiciciniyar walwale wannan sihiri wani irin mird'ewane akamasa
wani abun cikin wani hakan sukayita banye abubuwa daga karshe suna Kai karshen
kullin sekawai sukaga guntun takalmine dawani Kashi se dunkulin jini da babyn
roba mekamada wancan dattijon sak...suna gama bud'ewa maheerah tak'ona kayan.
Aiko zunbur abban mama dake kwance tin bayan tafiyarsu
yamik'e tsaye kamar Wanda aka tsikara duk seda suka bishi da kallo arazane Amma
Banda gimbiya halila daketa famar murmushi...shiko rik'e kanshi yayi dake juya
Mashi sosai kana yayi baya luuuuu ze Fad'i cikin sauri jalaludeen yataroshi
yafad'a jikinshi... d'agowa yayi Yana kallon gimbiya halila kamar zeyi kuka se
kawai ta girgizamai Kai alamar karyayi...shiru yayi Yana duban abbe nasu yakai kusan
minti 5 ahakan kamun gimbiya halila tacewa mero takawo ruwa ba musu kuwa mero
takawo mikawa jalaludeen tayi tana fad'ar kayi addu,a tukunnah kashafa masa a
fuska...hakanko akayi bayan yakarb'a yayi addu,ar kamar yadda tace kana yashafa
masa a fuska atake yasauke ajiyar zuciya me k'arfi kana yafara bud'e idonshi da
salati d'auke abakinshi yabud'e su tarr akan fuskar jalaludeen...yunkurawa yayi
zetashi jalaludeen yatemaka masa yatashi kana shiga k'arewa wurin kallo cikin
sauri jalaludeen yace abbe.
""Na,am jalal inamuke anan mimukeyi anan? Ina
alyasat?
"Alhmdllh alhmdllh alhmdllh shine kawai abunda kefitowa
daga bakin jalaludeen yabud'e baki zeyi magana kenan su bibibo suka bayyana
awurin yanad'auka mama...cikin sauri gimbiya halila tamik'e Wanda sukayi atare
itada jalaludeen miyasa meta maheer? Cewar gimbiya halila...karkidamu
tajigatane sabida matsalar da kasamu Amma komai lpy insha Allah..to alhmdllh
tafad'a tareda bashi wuri ya kwantarda ita... maheerah ce tashiga Basu lbrn
abunda yafaru acan dakuma yadda sukayida abunda suka d'auko...shidai jalaludeen
inbanda tasbihi ga ubangiji ba,abunda yakeyi...yayinda gimbiya halila tayi musu
Adda,a sosai dakuma fatan alkhairi taname jinjinawa kannen nata dasuka kasance
bayan sallah nagani☺️
""Nisawa tayi tana fad'ar aiki yayi kyau sosai
maheer domin abban zaraah yasamu lpy.. dukkansu murmushi sukayi hadda
jalaludeen shiko abbe biye kawai yakedasu Yana kallo domin Sam besan inda
kalamansu suka nufaba Kuma bayajin hausa garama jalal yad'an ji sabida zamanshi
Nigeria
Ganin irin kallonda yake musune yasa gimbiya halila fad'ar
sannu bawan Allah nasandai dukkanmu Nan baka sannumuba bancin wannan
Tanuna jalaludeen dake zaune kusanshi d'aga Mata Kai yayi
domin da larabci take magana shiyasa yafahimceta... cigaba tayida fad'ar to
abunda yafaru gaskiya wannan yarinyar itace silar had'uwarmu dakai tanuna mama
dake kwance kana tabashi lbrn tin lokacin da mama ta tahad'u dashi har izuwa
kawo yanzu da sihirin yabar jikinshi shera 4 kenan..seda takai karshe kana tace
kaji yadda akayi muka sameka har zuwan wannan bawan Allah yace Kai abbanshine..
Shiru kawai abbe yayi Yana sauraronta idonshi suncika Tabb
da k'walla Yama kasace komai se aikin kallon mama yake
Jalaludeen kuwa se murmushi yakeyi seda gimbiya halila tace
kagaya masa yadda kuka rasashi domin hankalinshi yak'ara kwanciya Nan ko
jalaludeen yabashi lbr iya abunda yasani na b'atanshi dakuma tashin hankalin da
ahalinsu suka shiga Amma ya boye masa cinwon ammy...awannan Karon kuka sosai
abbe keyi bawanda yahanashi domin dukkansu sunsan abunda ciwo sosai arabakada
ahalinka natsawon shekaru...ana cikin wannan halinne mama tafarka tana turo
baki gaba tana Kiran bibibo
*SOLDIERS FAMILY* complete ne ga duk me buk'atar complete
akwai ak'asa 💃
Murmushi sukayi atare kana bibibo tarik'ata tatashi zaune
kamun yace uwar gijiyata abbanki fa yasamu lpy...wani irin k'walalo Ido mama
tayi kamun tasaka ihun murna tamik'e aguje taje gun abbe dake zaune Yana
kallonta sekawai Tafad'a jikinshi tana abbana kawarkeko? Bazaka Kara ciwoba
insha Allah yanzu mikakeso abbana naje nasaka Biba takawoma? Jin yayi shiru
Kuma biyi Mata yadda yasaba ba seta d'ago tana dubanshi taga shid'in ma ita
yake kallo kunya taji takamata atake Kuma jikinta yayi sanyi data tuna yafa
samu lpy kardai ace yamantata janye jikinta tayi daga nashi zata Mike sekawai
taji yamaidata Yana shafa bayanta hawaye nazuba a idonshi godiya yakesan yimata Amma yakasa furta komai
se aikin shafa bayanta yakeyi Yana hawaye Koda ba,a bashi lbrn ta ba iya yadda
tayi yanzu da,akace yasamu lpy ya,Isa yanuna masa tsananin sonda take masa
shiko mizeyiwa wannan yarinya yabiyata aduniya...sunjima ahakan sosai kamun
yad'agata Yana fad'ar ngd ngd ngd sosai y'ata Allah yayimiki albarka Allah
yabaki ingattacciyar rayuwa Allah yabaki Ni,imar duniya data lahira Allah
yabaki miji nagari Wanda zekulada rayuwarki cikin amunci... dukkansu da ameen
suka amsa kana wurin ya keceda fira kowana bada lbrn abunda yasani kamun
haduwarshi da wani..!
Dubai
Suna kan hanyar zuwa d'aukar mlm Abba yakirasu yace suzo
yadawo ance suna nemanshi...to kawai sukace tareda K'arasawa suka d'auko mlm
pert d'in ammy sukakaishi inda sukace suhaif da alhusain sukaishi inda ammy
zasuje suga Abba...hakanko akayi bayan sunje gun Abba sunjima awurinshi suna
tattaunawa bayan sungama kana suka fito kowannen ji yakeyi kamar ancire masa
k'aya ajiki ahakan suka Isa pert d'in ammy suka samu mlm nazaune shida su Al
Hassan domin yaduba ammy har an mayarda ita d'aki wuri suka samu suka zauna..
Kana mlm yashiga yimusu bayi ""agaskiya ciwon
mahaifiyarku ba komai bane face babbak'un aljanu sune aka izo Mata Kuma
akowacce Rana ta duniya tsafi sukeyi ajikinta domin ba,abuk'atar tawarke Kuma
Basu tashi kashetaba ba,ba,abunda zance muku anan illa kudage da addu,a Kuma
akwai wasu addu,oi dazan Baku zaku Rika yimatasu da maganin dazan,arika yimata
wanka ana shafe mata jikinta sedaifa kusani abune me matuk'ar wahala rabatada
way'annan hatsabiban alajanun shiyasa nace kudageda addu,a....nisawa suhaif
yayi kana yace shikenan mlm mungode sosai Kuma insha Allah zamuyi yadda kace.
To allah yabata lpy...duk suka amsa da ameen shidai alyasat
Yama kasa magana domin inba lugudeba Babu abunda zuciyarshi keyi tinani yakeyi
wayayiwa mahaifiyashi wannan mummunan abun? Mita aikata agaresu da har
za,acutarda ita? Atake yaji komai na stet d'in yafara tsanarshi domin inba
nanba to wazemata wannan mugun aikin lallai shakka Babu duk Allah yatoni asirin
Wanda yayi Mata wannan abun to sedai uwarsa ta haifi wani wlh...wannan tinanin
dayakeyi shine yusif keyi hakama su Al,Hassan lateep dabaya boyone kawai
yafitarda nashi Ali bayan sunyiwa mlm rakiya sundawo kallonshi duka sukayi Jin
yafad'i abunda ke zukatansu kamun sumeke zuwa Shirin masalachi domin yau
jimu,a.
Dukkansu sunshirya cikin manyan Kaya na larabawa jallabiya
ce ajikinsu da hirami sunyi kyau matuk'a kamar kasacesu kagudu...shidai gogan
natse yagame fuska kamar besan minene dariyaba lateep ne yakalleshi kamun yace
kaikam matarka nada aiki bro wannan cin magani hakan humm lallai zatasha
fama...dariya suka saka atareda yusif yace Kai bro wato bama shine zesha famaba
ita? Eh mana lateep yafad'a Yana k'ara kallon alyasat d'aya Kara yaderai kamar
besan dashi sukeba...maganar lateep ce tamakale jin ana sanarwar an d'aura
auren shareef da muhibbat se najeeb da yusra sadeeq da Maryam se Kuma sulaiman
da ashnah dukkansu akan sadaki dubu d'ari Allah yabasu zama lpy..
Se a lokacin wani k'ayataccen murmushi ya bayyana akan
kyakkyawar fuskarshi Yana shafa kwantaccen sajenda yayiwa fuskarshi
kawanya..shiko lateep da yusif dariya sukayi lokaci d'aya ganin yadda fuskar
dake mutuk'e yanzu tawayeda anuri ahakan suka nufi gidan zuciyarsu fyass..!
Ghana
Shiru wurin yad'auka suna saurarar gimbiya halila inda take
cewa abbe""""bawan Allah bawai baka zaraah ne bamasanyiba
aa zaraah amanace awurunmu bamasan abunda zesakata kuka arayuwarta domin muma
wani gefene ita na rayuwarmu zamu iya isko zaraah aduk inda take afad'in duniya
sedai abunda ka,iya zuwa yadawo ne bamaso tinda har aka,iya yima wannan aika
aikar acikin jinsinku tofa ko zaraah wata Rana zasu iya cewa sucutarda ita....
""Idan ko hakan taru Sena k'ararda ahalin duk
Wanda yayi gangancin yin hakan cewar bibibo dake cika Yana batsewa..
""Nafahimceku Kuma insha Allah baza,asamu matsala
ba inaso na inganta rayuwarta acikin mutane Yan uwanta tinda rayuwa ajinsinku
bazeyuba Kuma nabaku dama na Kuma amunce ga duk Wanda yayi yunk'urin cutarda
ita m
Kuhukuntashi... shikenan zance yazo karshe cewar maheerah
dukkansu murmushi sukayi Banda jalaludeen daya Lula duniyar tinani Wai sune
kezauneda aljanu suna magana Baki da Baki kamar mutane Yan uwansu lallai inbaka
mutuba kallo bek'are makaba aduniya.
Kallo mama bibibo yayi yace uwar gijiyata aizakibi abbanki
ko? "Eh tafad'a ahnkali kamun tace to kufa? Dariya yayi kamun yayi magana
maheerah tace duk inda kike a fad'in duniya Muna taredake k'awata iyarai da
mutuwa..Aiko tawashe Baki tana dariya ahakan suka shiga jirginsu se garin Abuja
inda jalaludeen yabar wasu daga cikin tawagarsu subi gimbiya halila takaisu gun
way'anda sukazo nema ajeji captain Usman ne yajagoranci tafiyar..
Bayan saukarsu Abuja akashiga yiwasu abbe shirshiryen tafiya
shida mama domin basuda passport da visa...cikin kwana ukku aka gama komai inda
jirginsu yad'aga zuwa *Dubai* k'arfe 4pm jirginsu yasauka Al Hassan ne kawai
yasanda zuwan nasu domin Shi kad'ai jalaludeen yagayawa Aiko yayi kuka yayi
farin ciki marar misal tuwa Shi kad'ai yaje dokosu tin a filin jirgin dayaga
abbensu ya rungumarshi Yana kukan farin ciki dakyar abbe ya,iya Raba jikinshi
danashi kana yarungumi jalaludeen daganan suka shiga mota zuwa gida mama da
abbe ne abaya jalaludeen kuwa na gefen Al,Hassan ahakan suka shigo cikin stet
d'in Wanda tin daga babban Gert d'in shigowa stet d'in mama taware idonta tana
kallon abunda idanuwanta kegani wasu irin miyagun halittune masu ban tsoro da
firgici kowanne Yana sintiri asama da makamai ahannunsu kamar masu Shirin yak'i
wani mugun launi da kallar stet d'in kebadawa kamar hadari ya had'u irin me
Baki da jaa d'innan Kuma be saukoda ruwaba...cikin mmkin wannan tashin hankalin
datake gani suke tafe har suka K'arasa bakin pert d'in habibbty duk suka fito
nan ma kallon abunda ke faruwa tsakanin pert d'innan biyu takeyi wannan dasuka
tsaya dakuma wani dakecan gaba Wanda ba pert d'in kowa bane Sena ammy wasu
kalar launuka kefita daka kowanne part acikinsu gakuma wasu halittun nanma abun
tsoro ahakan abbe yarik'e hannunta ganin tayi tsaye suka shiga cikin perlon
habibbty..!
Tofa 🤔 wannan wanne irin abune ke faruwa acikin
wannan stet?
Shin minene alak'ar dake tsakanin mama dasu gimbiya halila?
Ina dangin mahaifin mama suke?
Shin suwaye kena hannun acikin wannan mummunan abun
da,akejifar ahalin habeeb shuraim dashi wato abbe?
Wanne irin zama mama zatayi acikin wannan stet d'in me
tattareda abubuwan mmki da Al ajabi bugu da Kari kartawan sojojin gidan taza
Kaya atsakaninsu?
Duk kubiyoni acikin *SOLDIERS FAMILY* Pat 2 danjin yadda
zata Kaya
Free page yak'are *SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500
kacal 👌 ga duk me buk'atar complete 700 Idan kinshirya siya Zaki iya
tuntub'ar wannan nomber 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan
nomber 👉 08107819124
Autar alheri ✍️
*S F*
No comments